Rundunar Ƴansandan Jihar Kebbi ta cafke wata mata ƴar shekara 20 wacce ake zargi da haifar jaririya sannan ta binne ta da rai a cikin gonar da ke garin Kamba, Ƙaramar Hukumar Dandi.
Kakakin rundunar, SP Nafi’u Abubakar, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Yuni, 2025, inda wacce ake zargin ta ɗaure wuyan jaririyar da zani guda uku tare da rufe bakinta, kafin daga bisani ta binne ta a cikin wani daji da ake kira Malam Yaro da ke Kamba.
- Gwamnatin Kebbi Ta Ba da Ƙwangilar Gina Hanyoyi Kan Naira Biliyan 2.1
- Manoma Na Neman Ɗauki Bayan Ambaliya Ta Lalata Gonakin Shinkafa A Kebbi
Sai dai wani mai gonar yankin, Alhaji Kabiru Muhammad Kamba, ya gano ramin da aka yi amfani da shi wajen binne jaririyar, inda ya sanar da al’umma kuma aka ceto jaririyar da ranta a ranar 26 ga Yuni. An garzaya da ita zuwa Asibitin Kamba, inda likitoci suka tabbatar da cewa tana cikin ƙoshin lafiya.
Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Sani Muhammad Bello, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen yaƙar cin zarafin yara. Ya kuma yi kira ga iyaye da al’umma da su ba da kariya ga ƙananan yara tare da kauce wa aikata irin wannan ta’addanci saboda talauci ko wasu dalilai.
CP Bello ya yaba wa matar gwamnan jihar, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, bisa kulawa da taimako da ta nuna wajen ɗaukar nauyin kula da jaririyar. Rundunar ta kuma tabbatar da cewa wacce ake zargi za ta fuskanci shari’a bayan kammala bincike a sashin manyan laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp