Rundunar ‘yansandan Edo ta kama wani matashi dan shekara 16 da laifin lalata wata yarinya ‘yar shekara 2.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Edo, Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da kama shi, ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne a unguwar Egba da ke Karamar Hukumar Uhunwonde a ranar 7 ga watan Yuni.
- “‘Yan Siyasa Ne Aka Bai Wa Gidaje Ba Malaman Makaranta Ba A Kano”
- Kotu Ta Umarci DSS Ta Bai Wa Emefiele Damar Ganin Lauyansa Da Iyalinsa
Sashen kula da jinsi na sashen binciken laifuka na gudanar da bincike kan lamarin. Nwabuzor ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Da ‘yan jarida suka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce;
“Yarinyar ‘yar shekara biyu takan zo wajen kanwata. Ta zo a wannan rana, sai na ce mata ta koma gida cewa kanwata ba ta gida amma ta ki tafiya.
“Don haka, sai na dauke ta, na kwantar da ita a kan gadon, amma a lokaci ni ban kusance don yin lalata da ita ba, sai kawai na sanya al’aurata a tsakanin cinyarta.
“A wannan lokacin ban san abin da ya faru ba kuma ban san abin da ya same ni ba saboda ban taba yin wani abu makamancin hakan a baya ba.”