Wata majiya mai tushe da ta tsegunta wa jaridar LEADERSHIP HAUSA a Kano wacce kuma ta hana a bayyana sunanta ta ce gaskiyar lamari gwamnatin baya ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje ‘yan siyasa ta bai wa gidaje da sunan malaman makaranta, domin kuwa sharadin da aka san a biyan kashi 10 ciki 100 malamai ba su da shi.
Majiyar ta ce gidan sun kai sama da miliyan tara wanda ba a samu malamin da ya iya cike sharudan ba. Majiyar ta ce a iya saninta ba ta san malami ko daya ba da ya samu wannan gida da aka ce an bai wa malaman makaranta a Kano.
- Cire Tallafin Mai: Farashin Kayayyaki Ya Karu Da Kashi 22.41
- Sin: Bai Kamata A Shigar Da Salon Fito-na-fito Cikin Tsarin Ayyukan Hukumomin Hada-hadar Kudi Na Kasa Da Kasa Ba
A ceawar majiyar, tunaninsu da zarginsu ‘yan siyasa ne kawai suka amfana da gidajan, amma ba malaman makaranta ba kamar yadda gwamnatin Ganduje ta ce ta yi.
Kan haka ne majiyar ta yi kira da sabon gwamnan Kano, Injiya Abba Kabir Yusuf da ya gaggauta gudanar da bincike a kan lamarin. Majiyar ta kira lamarin da badakkala da yaurar malaman makaranta da aka ce an tsara gina gidaje 5000 har ma an bai wa wasu malaman makaranta.
A karshe dai kan wannan zargin wakilinmu ya yi iya kokarisa domin jin ta bakin masu ruwa da tsaki kan lamarin, amma lamarin ya ci tura har zuwa hada wannan rahoto.