Rundunar ‘yansandan a Jihar Ogun ta kama wani yaro dan shekara 17 mai suna Jamiu Adebayo da laifin lalata da ‘yar makocinsa ‘yar shekara takwas a unguwar Aregbe dake Abeokuta, babban birnin jihar.
Jaridar PUNCH Metro ta gano cewa wanda ake zargin ya yaudari yarinyar zuwa dakin iyayensa, inda ya umarce ta da ta cire mata rigarta, sannan ya yi lalata da ita.
- Yadda Kuncin Rayuwa Da Matsalar Tattalin Arziki Ke Kara Haifar Da Rikice-rikice Tsakanin ‘Yan Haya Da Masu Gidaje
- Jarumin Bollywood Saif Ali Khan Ya Tsallake Rijiya Da Baya
Rundunar ‘yansandan ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin, kuma ana ci gaba da gudanar da kwakkwaran bincike don gano musabbabin aikata laifin.
PUNCH Metro ta samu labari daga mai magana da yawun ‘yansandan, Omolola Odutola, cewa mahaifiyar wacce aka lalata, mai suna Olabode, ba ta nan a lokacin da makota suka kira ta domin sanar da ita cewa jini na fita daga al’aurar ‘yarta.
Rundunar ‘yansandan ta ce Olabode ta shaida wa ‘yansanda cewa ta yi matukar kaduwa da fargaba a lokacin da ta gano jini na fita daga al’aurar ‘yarta a lokacin da ta isa wurin.
A kokarin da wakilinmu ya yi na gano musabbabin zubar jinin, ya gano cewa, duk kokarin da aka yi na shawo kan yarinyar ta bayyana abin da ya faru ya ci tura, domin ta sha nanata irin wannan bayanin da ta yi wa makotanta cewa itace ta raunata al’aurarta. .
Bayan matsin lamba da lallashi, an ruwaito wacce abin ya shafa ta shaida wa mahaifiyarta cewa wani matashi mai suna Adebayo mai shekaru 17 da ke zaune a ginin makota ne ya yi mata fyade.
Rundunar ta bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da shi inda ya shigar da ita cikin dakinsu, inda ake zargin ya hau kanta ya yi lalata da ita.
Odutola ya ce, “Wadanda ake zargin ya dauke ta zuwa bandakinsu domin ta wanke jinin, sannan ya umarce ta da ta sauya rigarta. Ya kuma lallashe ta kan ta yi karya wai sanda ce ta yi mata rauni a al’aurarta.
“Jami’an tsaro sun yi gaggawar kama wanda ake zargin. An bayar da fom na likita ga wacce abin ya shafa da mahaifiyarta don a duba su kuma su ba da rahoto. A halin yanzu ana gudanar da bincike na farko.”