Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (NSCDC) a Jihar Ribas a ranar Talata ta gabatar da wasu mutane 16 da ake zargin barayin mai ne da laifin tace danyen mai ba bisa ka’ida ba domin samar da dizal.
Kwamandan rundunar ‘yansandan jihar, Mista Michael Ogar, ya gurfanar da mutanen 16 a gaban manema labarai a Fatakwal.
- Majalisar Dokokin Kano Ta Amince A Sauya Sunan Jami’ar KUST Zuwa Sunan Dangote
- Maulidi: Kungiyoyin Mata Sun Yi Taro Kan Muhimmanci Koyi Da Fiyayyen Halitta SAW A Abuja
Ya ce jami’an NSCDC da na ruwa na Nijeriya sun kama su ne a wani samame daban-daban a wurare daban-daban a jihar.
A cewarsa, sun kwace kimanin lita 200,000 na gurbataccen dizal da ake shirin rabawa masu ababen hawa a jihar.
“Takwas daga cikin wadanda ake zargin jami’an NSCDC na sashin yaki da barna ne suka kama su yayin da sauran takwas din kuma sojojin ruwa na Nijeriya da ke Fatakwal ne suka mika mana su.
“An kama mutane 16 da ake zargin suna da hannu wajen satar mai da kuma tace man dizal ba bisa ka’ida ba.
“An kama wasu daga cikin wadanda ake zargin sun kwashe kimanin lita 200,000 na dizal tare da manyan motocinsu, motocin wasanni da sauran motoci zuwa wurare daban-daban a cikin jihar kafin a kama su,” in ji shi.
Ogar ya ce rundunar ta kama wasu da dama tare da kwace albarkatun man fetur biyo bayan umarnin da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola da Gwamna Nyesom Wike na Ribas suka yi bai NSCDC.
Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa, rundunar ba za ta huta ba har sai an dakatar da duk wani nau’i na fasa kwaurin man fetur ba bisa ka’ida ba da barnata ayyukan man fetur da iskar gas a jihar.
“Ba za mu yi sulhu a kan aikinmu ba. Yawan kama su na nuna cewa jami’anmu da mutanenmu suna bin umarnin gwamnati na dakatar da barnace-barnace.
“Baya ga wannan, muna kuma bin masu gidajen mai da ke hada baki da masu aikata laifuka ta hanyar ba su damar amfani da gine-ginensu da kayan aikinsu wajen tara man fetur ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa, “Rundunar ta tana bin irin wadannan masu gidajen man, kuma za ta kama su tare da gurfanar da su a gaban kuliya saboda sun bari an yi amfani da kadarorinsu wajen aikata haramtattun ayyuka.”
Kwamandan ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya yayin da rundunar za ta nemi gwamnatin tarayya ta kwace motocin da man fetur din da ta kama.