Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wani tsohon dan wasan kwallon kafa, Okafor Emmanuel Junior, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, bayan isowarsa daga Sao Paulo, Brazil a jirgin Addis Ababa na kasar Ethiopia.
An cafke Junior ne dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.40 wacce ya boye a cikin jakar kayanshi.
An kama matashin mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Arochukwu, jihar Abia ne a ranar Litinin 26 ga watan Satumba, bayan da jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi suka gano cewa ya boye hodar a cikin jakarsa.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce, yayin wata tattaunawa ta farko da aka yi da shi, Okafor ya bayyana cewa, tsohon dan wasan kwallon kafa ne na kungiyar asibitin koyarwa na jami’ar Enugu FC, inda ya yi wasa har na tsawon shekaru hudu kafin ya tafi kasars Sri Lanka a 2014.
“Ya kara da cewa ya koma Brazil ne daga Sri Lanka, ya buga wasa na tsawon shekaru biyu amma bai samu nasarar ci gaba da wasan kwallon kafan ba a Brazil saboda rashin takardun hukuma,” in ji Babafemi.