Rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fyade a jihar.
Kwamishinan ‘yansanda, Ahmad Magaji-Kontagora ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
- Ranar Malamai ta Duniya: Aikin Malanta A Zamanin Nan A Nijeriya
- Atiku Ya Karbi Mutane Dubu 25 Da Suka Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP A Bauchi
Ya ce wadanda ake zargin sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara takwas fyade yayin da dayan kuma ya yi wa ‘yar uwarsa mara hankali fyade.
“Wani Danjuma Tanko mai shekaru 30 da ke kauyen Zariya Kala-Kala, a karamar hukumar Koko/Besse, ya dauki wata yarinya ‘yar shekara takwas da ta ke siyar da wainar wake a gidan wani Umaru Dauda, inda ya yi lalata da ita da karfin tsiga. Ya sadu da ita ya ba ta N200.
“Wanda ake zargin ya bai wa Dauda N200 saboda amfani da dakinsa wajen aikata lalatar.”
Kwamishinan ya tabbatar da cewa a ranar 16 ga watan Satumba, da misalin karfe 1:00 na rana, wanda ake zargin, ya dauki ‘yar uwarsa marar hankali ya kai ta magudanar ruwa tare da yin lalata da ita ta karfi.
Ya kuma bayyana cewa, fyade na biyu da ake zargin wani Bashir Ibrahim na garin Kangiwa ne ya aikata a ranar 26 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan yin bincike.
Magaji-Kontagora, ya shawarci ’yan Nijeriya da su rika sanya ido a kan wuraren da suke kewaye da su domin dakile aukuwar irin wannan lamari tare da taimaka wa rundunar da bayanai masu amfani kan wadanda ake zargi.