‘Yansanda a jihar Jigawa sun cafke wani maigida da matarsa bisa zarginsu da bizne ‘sabuwar jaririyarsu da ranta.
Ma’auratan sun fito ne daga karamar hukumar Kiyawa a cikin jihar ta Jigawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar DSP Lawan Shisu Adam wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin a cikin sanarwar da ya fitar a jihar ya ce, bayan da rundunar ta samu rahoton afkuwar lamarin, sai ta tura jami’anta zuwa gurin da abin ya auku.
DSP Lawan ya ci gaba da cewa, uwar jaririyarsu ‘yar shekara 30 mai suna Balaraba Shehu da ke da zama a kauyen Tsurma da kuma mijinta mai suna Ahmadu Sale wanda aka fi sani da Dankwairo mai shekaru 25, sun hada kai da matarsa sun kashe jaririyarsu ta hanyar bizne ta da ranta ganin cewa, ba su shirya zuwan jaririyar ba.
A cewar DSP Lawan, jami’an mu da zuwan su gurin da abin ya faru, sun tsamo jaririyar daga cikin masai da uwar jaririyar ta bizne ta a ciki.
Ya ce, kwamishinan rundunar Emmanuel Ekot Effiom, ya bayar da umarnin a tura maganar zuwa ga sashen jami’an tsaro na SCID da ke a garin Dutse domin su gudanar da dogon bincike akan lamarin, inda ya ce, da zararar sun kammala binciken za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci shari’a.