Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama wasu yara matasa biyu da laifin yin fashi a wani kantin sayar da wayar salula guda 100 da na’urar jin waka guda 75 da dai sauransu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Ahmed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa aikin kamen ya biyo bayan rahoton sata da mai shagon ya kai.
- NSCDC Ta Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga A Kano
- Kashi 4.1 Na ‘Yan Nijeriya Ne Kawai Za Su Amfana Da Tsarin Mafi Karancin Albashi —Bankin Duniya
Ya kuma jaddada cewa da samun rahoton ne jami’an ‘yan sanda suka fara gudanar da bincike a kan lamarin, wanda ya kai ga cafke wasu dalibai biyu na makarantar sakandare ta Bakari Dukku.
PPRO ya kara da cewa da aka kama wadanda ake zargin, suka amsa cewa sun samu makullin kantin ne daga inda mai shagon ya ajiye.
Wadanda ake zargin sun kuma bayyana wa ‘yan sanda cewa sun sayar da wasu daga cikin wayoyin kan kudi Naira 5,000 da Naira 8,000.
Wakil ya bayyana cewa, “Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan ya umurci tawagar ORP karkashin jagorancin CSP Kim Albert da su gudanar da bincike. Binciken ya kai ga cafke Hamza Sadik, namiji mai shekaru 15 da Adamu Ahmadu, mai shekaru 15. Dukkanin mutanen biyu daliban makarantar sakandaren Bakari Dukku ne.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa cewa sun samu nasarar samun makullin shagon ne daga inda aka boye shi, sannan suka tsayar da lokacin da mai shagon zai tafi kasuwar kauyen, sannan suka bude kofar shagon domin yin sata da rana.
“Wadanda ake zargin sun sayar da kayayyakin da aka sace a kan farashi mai rahusa, daga Naira 8,000 zuwa Naira 5,000. An yi amfani da kudaden da aka samu wajen sayan tufafi, abinci, da wayar salula, wanda daga baya kuma aka sace wasu kayan daga hannun daya daga cikin wadanda ake zargin.”
Ya kara da cewa wasu daga cikin abubuwan da aka sace sun hada da “wayoyin hannu 21, MP4 MP4, caja daya, da makullin karfe daya, daga hannun wadanda ake zargin.”
Yayin da yake jaddada kudirin rundunar ta yaki da miyagun laifuka, Wakil ya ce za a mika wadanda ake zargin zuwa gidan kaso domin gyaran hali bayan kammala binciken da ake yi.