Rundunar ‘yansandan birnin tarayya, Abuja ta ce ta ceto mutum 58 da aka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da kakakin ‘yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar, ta bayyana cewa an ceto mutanen ne daga dajin Udulu da ke Karamar Hukumar Gegu ta Jihar Kogi, wanda ke da iyaka da Dajin Sardauna na Jihar Nasarawa.
- Matatar Man Dangote Za Ta Fara Aiki A Ranar 22 Ga Watan Mayu
- Allah Ya Yi Wa Jarumin Kannywood, Mai Mala Rasuwa
Ta kara da cewa akwai wasu da aka ceto daga wasu sansanonin ‘yan bindiga da mutanen da aka gano a wasu wurare a Abuja.
“A lokacin da barayin suka ga jami’an tsaro karkashin jagorancin ‘yansanda, sai suka soma harbin su wanda hakan ya ja aka yi musayar wuta.
“An fi karfin ‘yan bindigar inda suka tsere da raunukan harsasai a jikinsu tare da barin wadanda suka sace,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa a lokacin aikin ceton, daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su mai suna Tama Jonathan ya rasu sakamakon raunukan da ya samu, inda ya mutu a wurin nan take.
“An kai wa iyalinsa gawarsa domin a birne shi, sauran mutum 58 ana duba su a asibiti kuma za a hada su da iyalansu,” in ji sanarwar.
Rundunar ‘yansandan ta bayyana cewa ta gudanar da wannan aikin ceton ne tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro da ‘yan bijilanti, duk a yunkurin kawo karshen garkuwa da mutane.