Hukumar kula da ayyukan harba kumbuna masu dauke da mutane ta kasar Sin ta sanar da cewa, da misalin karfe 10:44 na safiyar yau 5 ga watan Yunin shekarar 2022 bisa agogon Beijing, an harba roka samfurin “Long March 2F” dauke da kumbon Shenzhou-14 a cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan.
Bayan kimanin dakika 577, kumbon Shenzhou-14 ya yi nasarar rabuwa da rokar tare da shiga hanyar da aka tsara, ‘yan sama jannatin dake cikin kumbon suna cikin yanayi mai kyau, kuma an cimma cikakkiyar nasara kan wannan aiki.
Wannan aiki shi ne karo na 23, tun bayan da aka kaddamar da ayyukan harba kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati na kasar Sin, shi ne kuma karo na 3 da aka gudanar da aikin a matakin tashar sararin samaniya.
Bayan da kumbon ya shiga hanyar yadda ya kamata, bisa yadda aka tsara, zai hadu da sauran sassan dake tashar sararin samaniyar. Nan gaba kuma, ‘yan sama jannatin za su shiga babban akwatin Tianhe, don soma zama a ciki na tsawon watanni 6, inda za su gudanar da wasu ayyukan da suka shafi kiyayewa da kula da dandalin tashar, da sarrafa hannayen mutum-mutumi, da fita daga akwatin, da ma wasu gwaje-gwajen kimiyya da fasahar sararin samaniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)