Kwanan baya ne, aka rufe taron kasashen da suka daddale yarjejeniyar tsarin MDD kan sauyin yanayi karo na 28 wato COP28, inda aka cimma yarjejeniya mai ma’anar tarihi, wadda a ganin kafofin yada labaru na kasa da kasa, an sha wahalar cimmawa.
Wannan shi ne karo na farko da aka cimma daidaito kan dakatar da yin amfani da makamashin kwal da sauran burbushin halittu. Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito cewa, a karo na farko kasashen duniya sun yarda da dakatar da yin amfani da makamashin kwal da sauran burbushin halittu cikin shekaru kusan 30 da ake gudanar da tarukan kolin MDD kan sauyin yanayi.
An yi nuni da cewa, dalilin da ya sa aka cimma wannan yarjejeniya mai ma’anar tairhi a taron COP28 shi ne, domin kasashen Sin da Amurka sun hada kansu, musamman ma shugabannin kasashen 2 sun kara azama kan hadin gwiwa. A yayin da shugabannin kasashen 2 suka gana da juna a San Francisco, sun jaddada aniyarsu ta sa kaimi kan samun nasarar gudanar da taron na COP28, lamarin da ya kara kuzari kan yadda kasashen duniya suke daidaita matsalar sauyin yanayi. (Tasallah Yuan)