• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Dakatar Da Kociyan Mata Na Leicester City Kan Zargin Yin Soyayya Da ‘Yar Wasa

by Muhammad
2 years ago
Leicester

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata ta Leicester City ta fara bincike kan manajan tawagar Willie Kirk, game da zargin yana soyayya da wata daga cikin ‘yan wasansa.

TRT Afrika Hausa ta  ce, Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Leicester ta dakatar da manajan sakamakon zargin, yayin da take gudanar da bincike kan batun. Don haka ba zai jagoranci tawagar a wasansu na Asabar ɗin nan ba.

  • Birmingham City Ta Kori Rooney A Matsayin Kocinta
  • Kocin Super Eagles Jose Peseiro Ya Ajiye Aikinsa Bayan Karewar Kwantiraginsa

Ƙungiyar ta fitar da sanarwa mai cewa “Willie Kirk yana taimaka wa kulob ɗin wajen gudanar da binciken na cikin gida, inda za a fito da sakamakon bincike a gaba”.

Sanarwar ta ƙara da cewa a yanzu mataimakiyar manajan ƙungiyar, Jennifer Foster da kuma mai horar da tawagar Stephen Kirby, za su ɗauki ragamar ƙungiyar a wasansu na yau da za su kara da ƙungiyar Liverpool ta mata.

Shi dai kocin da aka dakatar, Willie Kirk ya karɓi ragamar Leicester ne tun watan Yuli na 2022, lokacin da aka naɗa shi daraktan wasanni na ƙungiyar.

LABARAI MASU NASABA

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Daga bisani ya zama manajan ƙungiyar ranar 3 ga watan Nuwamba, inda ya maye gurbin Lydia Bedford.

A baya ma, Kirk ya taɓa jagorantar ƙungiyar Hibernian Women ta mata, da Preston ta maza, da kuma Bristol City, da ma Everton, kafin ya koma Leicester.

Haka nan kuma, ya taɓa zama mataimakin kocin Manchester United na ɗan lokaci a shekarar 2018.

A yanzu dai Leicester tana mataki na bakwai a teburin Women Super League ta Ingila, da maki 16 bayan wasanni 15. Kuma a yau za ta fuskanci Liverpool da ke mataki na biyar a gasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax
Wasanni

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86
Da ɗumi-ɗuminsa

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
Wasanni

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Next Post
Mahaifin Matar Gwamnan Neja, Sarkin Malami Nupe Ya Rasu Yana Da Shekaru 90

Mahaifin Matar Gwamnan Neja, Sarkin Malami Nupe Ya Rasu Yana Da Shekaru 90

LABARAI MASU NASABA

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

Jerin Gwarazan Taurarinmu!

November 7, 2025
‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura

November 7, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

Gwamnatin Zamfara Ta Ɗauki Malaman Makaranta 500 Aiki

November 7, 2025
GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja

November 7, 2025
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

November 7, 2025
Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.