Alhaji Muhammad Egba Enagi (Sarkin Malami Nupe), hakimin kauyen Dikko-Enagi da ke karamar hukumar Edati a jihar Neja ya rasu.
Marigayi Enagi mai shekaru 90, wanda ya rasu a daren ranar Asabar, shi ne mahaifin Uwargidan Gwamnan Jihar Neja, Hajiya Fatima Bago, da kuma tsohuwar uwargidan Gwamnan Jihar, Sanata Zaynab Kure.
- ‘Yan Ƙwadago Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai-baba-ta-gani A Neja
- ‘Yan Adawa Ne Suka Tunzura Mutane Yin Zanga-zanga A Neja Da Kano – APC
Marigayi Enagi mutum ne mai ilimi kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati. Ya yi ritaya a matsayin Babban Sakatare a kauyensu da ke Dikko-Enagi a karamar hukumar Edati ta Jihar a shekarun 1980.
Talla
Za a yi jana’izar marigayin a yau Lahadi da misalin karfe 2 na rana a gidansa da ke Dikko-Enagi, karamar hukumar Edati ta jihar Neja.
Talla