‘Yan Nijeriya sun yi asarar sama da naira biliyan 93.72 sakamakon ayyukan zamba a tsakanin watan Janairun 2023 zuwa Disamban 2024.
Wannan ya kai ga adadin asarar sama da naira 1, 005,170,000,000 da aka tafka a cikin shekaru 25.
‘Yan damfara da masu zamba cikin aminci na ci gaba da vullo da sabbin dabaru da hanyoyin yadda za su cuci jama’a duk kuwa da yawan wayar da kan jama’a da ake yi na hanyoyin da za su bi wajen kauce wa masu irin wannan ta’asar.
- Me Ya Sa Fursunoni Masu Jiran Hukuncin Kisa Ke Ƙara Cunkoso A Gidajen Yarin Nijeriya?
- Abuubuwan Da Suka Fi Daukar Hankalin ‘Yan Nijeriya A 2024
A Disamban 2022, Darakta a sashin Inshura ta Nijeriya (NDIC), Michael Oladele, ya shaida yadda jama’a ke tafka dimbin asara sakamakon aikace-aikacen damfara da zamba a cikin kasar Nijeriya.
A lokacin ya shaida cewar adadin kudi naira biliyan 911.45 ne aka yi asararsu a cikin shekaru 23, inda ya ce, babu shakka asarar wannan makudan kudaden ya gurgunta tattalin arzikin wadanda lamarin ya shafa da kuma tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2024, wani mai suna Chinedu Okoronkwo an gurfanar da shi a gaban babban kotun tarayya da ke Enugi, bisa zarginsa da ayyukan damfara ta kamfanin ‘Reliance Microfinance Cooperative Society Limited’ inda ya damfari masu zuba hannun jari naira miliyan 71.58.
Zuwa watan Oktoban 2024, harkokin damfara ya shafi ‘yan Nijeriya miliyan 2.7 da suka rasa naira biliyan 89.4 kan masu damfara ta BBHTV. Duk da kuwa gwamnatin tarayya ta kulle asusun bankunan BBHTV da dama.
Watanni biyar kacal da fara aiki, BBHTV ta sanar da wadanda abin ya shafa cewa hukumar tattara kudaden shiga ta tarayya (FIRS) ta rufe asusun ta da dama.
Masu gudanar da shirin asusun sun yi ikirarin cewa wadannan rufaffun asusu na da jimillar naira biliyan 89.4.
Sakamakon karuwar wadannan ayyukan damfara, majalisar dattawa ta zartar da dokar saka hannun jari da tsare-tsare (ISB) 2024, don maye gurbin dokar zuba jari da tsaro ta 2007, domin dakile aniyar masu zamba da damfarar mutane.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin manyan kasuwanci, Osita Izunaso, ya ce kudirin dokar zai kare mutuncin tabbatar da tsaro daga duk wani nau’in cin zarafin ‘yan kasuwa, kyautata tsaron kasuwanci, hana cin hanci da rashawa, haramtattu ayyuka, zamba da kuma rashin adalci a harkokin kasuwanci da suka shafi harkokin zuba jari.