ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwarzon Gwamnan 2024 – Alhaji Abba Kabir Yusuf

by Leadership Hausa
2 years ago
Gwarzo

Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo ta Gwarzon Gwamnan Shekarar 2024 ta Jaridar LEADERSHIP, saboda gagarumin aikin da ya yi a fannin ilimi da sauran muhimman bangarorin ci gaba a Jihar Kano

Gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci kan ilimi tare da ware kashi 31 na kasafin kudin jihar na Naira biliyan 570, kwatankwacin Naira biliyan 165.4, a bangaren ilimi. Wannan matakin na nufin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, wadda Kano ce ke kan gaba na mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, da kuma bai wa yara marasa galihu damar samun ingantaccen ilimi.

  • Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
  • Dubun Wata Budurwa Da Wasu 5 Ya Cika Bayan Ta Sace Wayoyin Salula 30 Na Matan Aure A Kano

Gwamna Yusuf ya yi sabbin gine-gine a makarantu, ya samar da kujeru da tebura da sauran kayan karatu. Haka kuma, gwamnatinsa ta bayar da tallafin karatu ga matasa maza da mata da yawa don yin karatu a kasashen waje, don tabbatar da cewa ilimi ya zama ginshikin ci gaban jihar.

ADVERTISEMENT

Shahararsa da kalaman “ilimi, ilimi, ilimi” sun tabbatar da cewa bangaren ilimi shi ne abin da ya fi bai wa fifiko.

An haifi Alhaji Abba Kabir Yusuf a gidan Sarautar Fulanin Sullubawa, wanda suke wani tsagi ne daga sarakunan Masarautar Kano. Ya yi kuruciyarsa a Gaya, a hannun kakansa, Alhaji Yusuf Bashari, Hakimin Gaya. Ya yi karatunsa na Firamare da Sakandire a Kano kafin samun difiloma a Fannin Injiniyan Ruwa da Muhalli a Kwalejin Fasaha ta Mubi da Kaduna Polytechnic.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare

Daga baya, Gwamna Yusuf ya samu shaidar digiri a fannin gudanarwa a Jami’ar Bayero ta Kano. Abba Kabir Yusuf ya fara aikinsa a Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, inda ya samu gogewa a fannin aikin gwamnati. Har ila yau, ya taba rike mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na Cibiyar Shirye-shiryen Ilimi da Gudanarwa ta kasa.

A siyasance, Abba Kabir Yusuf ya fara aikinsa a karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya rike mukamai daban-daban, ciki har da mataimaki na musamman da mukamin sakatare na musamman da mukamin babban sakatare, da kuma Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na Jihar Kano.

A shekarar 2018, ya tsaya takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP, wanda daga nan ne ma ya samo lakabin sunan “Abba Gida-gida.” Duk da cewa bai yi nasara ba a wancan lokacin, amma bai karaya ba. A shekarar 2023, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP tare da Jagoransa Sanata Kwankwaso, kuma ya lashe zaben gwamnan jihar.

Bayan lashe zaben, Abba Kabir Yusuf ya fuskanci kalubale na siyasa, ciki har da soke zabensa a kotun sauraron kararrakin zabe. Sai dai, ya daukaka kara zuwa Kotun Koli, inda aka tabbatar da zabensa a matsayin gwamnan jihar a watan Janairu 2024. Wannan karfin hali da juriya da ya nuna sun kara masa daraja a matsayin shugaba wanda ba ya barin wani abu ya shagaltar da shi daga kokarin ciyar da jiharsa ta Kano gaba.

A wajen inganta rayuwar al’ummar Kano kuwa, Gwamna Yusuf yana gina sabbin gadoji a Kofar Dan Agundi da Tal’udu, domin rage cinkoson ababen hawa a jihar. Haka kuma, ya inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da kayan aiki da magunguna a asibitoci kyauta. Gwamnatinsa ta kuma kaddamar da shirin tallafa wa mata 5,200 da kudi Naira 50,000 a matsayin jari. Wannan tallafi na nufin taimaka wa mata wajen karfafa wa kasuwancinsu da rage talauci a tsakaninsu.

Haka kuma, gwamnatinsa ta canza fitilun kan titunan Kano zuwa masu amfani da hasken rana, wanda ya sanya titunan jihar zama cikin haske ko yaushe tare da rage amfani da makamashi mara tsafta. Gwamna Yusuf yana biyan albashi, fansho, da kudin sallama akai-akai, kuma ya kasance cikin gwamnonin farko a Nijeriya da suka fara aiwatarwa da biyan mafi karancin albashi na Naira 71,000. Bugu da kari, gwamnatinsa ta biya bashin Naira biliyan 3.5 na kasashen waje da Naira biliyan 60 na cikin gida, ta rage bashin jihar zuwa Naira biliyan 127.8 a tsakiyar shekarar 2024.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zama jajirtaccen gwamna wanda ya yi fice wajen kawo sauyi a fannin ilimi da lafiya da gine-gine da kuma tallafa wa jama’a. Jagorancinsa ya zama abin misali a Nijeriya, burinsa bai wuce sanya murmushi a fuskar Kanawa ba.

Gwarzo
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

July 23, 2026
Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare
Labarai

Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare

July 23, 2026
Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?

July 23, 2026
Next Post

Nijeriya Ta Jaddada Aniyarta Ta Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Yammacin Afirka

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma Sama Da 20 A Zamfara – Amnesty International

July 23, 2026
Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare

Sarkin Katagum Ya Jagoranci Addu’ar Roƙon Ruwa A Azare

July 23, 2026
Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?

Me Ya Sa Ra’ayin Duniya Ke Karkata Zuwa Sin Yayin da Tasirin Amurka Ke Faduwa?

July 23, 2026
Cire Tallafi: Majalisar Nasarawa Za Ta Binciki Yadda Aka Karkatar Da Kayan Tallafin Jihar

Gwamnan Nasarawa Ya Sallami Kwamishinoni Shida Na Majalisar Zartarwar Jihar

July 23, 2026
Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP,  Sun Kashe ’Yan Ta’adda 20 A Yobe

Rashin Tsaro: Tinubu Ya Amince Da Kafa Sabuwar Bataliyar Sojoji A Jihar Kwara

July 23, 2026
Akpabio

Tinubu Ya Dukufa Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro — Akpabio

July 23, 2026
Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

Taron AI Na Duniya: Kaya Ya Kwance A Tushen Kaba

July 22, 2026
Inganta Makarantu: Gwamna Lawal Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Gyaran Ilimi A Zamfara

Inganta Makarantu: Gwamna Lawal Ya Sanya Hannu Kan Dokokin Gyaran Ilimi A Zamfara

July 22, 2026
An Kaddamar Da Taron Kasa Da Kasa Na Bunkasa Hanyar Siliki Ta Dijital Na 2026

An Kaddamar Da Taron Kasa Da Kasa Na Bunkasa Hanyar Siliki Ta Dijital Na 2026

July 22, 2026
Amit Bhatia Na Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Sayen Kaso 30 Na Liverpool FC

Amit Bhatia Na Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Sayen Kaso 30 Na Liverpool FC

July 22, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.