Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Garin Kwale a Karamar Hukumar Ndokwa ta Yamma a Jihar Delta ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari saboda samun su da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Kotun da ke karkashin mai shari’a O. F. Enenmo, ta yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari saboda samunsu da laifin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
- Za A Sake Maka Ganduje A Kotu Kan Badaƙalar Naira Biliyan 57.4
- DSS Ta Musanta Kai Samame Ofishin NLC Kan Zanga-zangar Yunwa
Wadanda ake tuhumar, Mista Joshua Anamali, mai shekaru 25, da kuma Mista Nelson Adoh, mai shekaru 30, suna tsare a gidan yari na Kwale.
‘Yansanda sun kama wadanda ake tuhumar biyu ne a lokacin da suka saba tsayawa da bincike a ranar 27 ga watan Janairu, 2021, a Ndemili da ke Karamar Hukumar Ndokwa ta Yamma a Jihar Delta.
Alkalin da ya yi nazari kan karar da ake tuhumar wadanda ake zargin inda ya same su da laifi kuma a sakamakon haka ya yanke musu hukuncin daurin shekara 10 bisa laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Da take magana da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin, lauya mai shigar da kara, Misis Catherine Oboreruomo, ta yaba da hukuncin.
Oboreruomo ta ce, “Shaidu biyu sun bayar da shaida a shari’ar da ake tuhumar.
“Muna rokon matasa da su guji aikata laifuka saboda sakamakon laifuka shi ne hukunci.”