Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta kai samame ofishin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) da ke Abuja a daren ranar Laraba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa jami’an DSS sun kai samame shelkwatar NLC.
- Jami’an Tsaro Sun Yi Wa Ofishin NLC Dirar Mikiya Don Neman Hujja Kan Zanga-zangar Yunwa
- Gwamnatin Tinubu Na Ƙoƙarin Gyara Kurakuran Baya, Ba Jawo Wahala Ba – Minista
A cewar kungiyar, jami’an tsaron sun kai samamen ne da misalin karfe 8:30 na daren Laraba.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC, Benson Upah, ya ce, “Sun kutsa kai ne suka yi awon gaba da wasu litattafai a hawa na 2 sannan suka kwashe tarin wasu takardu.
“Jami’an sun yi ikirarin cewa suna neman kayan da aka yi amfani da su a zanga-zangar #EndBadGoveranance.”
Sai dai mai magana da yawun hukumar DSS, Dokta Peter Afunanya, yayin da yake mayar da martani, ya ce jami’an hukumar ba su kai wani samame a ofishin NLC ba.
A cewar sa, “Hukumar DSS ba ta kai samame ofishin NLC da ke Abuja ba.”