Wata Kotun Majistare da ke Igbosere da ke zamanta a Ebute-Metta, ta yanke wa wani mai hidima a wani gida, Emmanuel Robson, hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, bisa samunsa da laifin satar wasu makudan kudi daga wajen aikinsa.
Alkalin kotun mai shari’a Oluwatosin Erinle ya yanke wa Robson hukuncin ne bayan ya amsa laifuka 15.
- Kungiyar Masu Masana’antu Ta Nemi Gwamnati Ta Daidaita Harajin Da Ake Kakaba Musu
- Sabon Salon ‘Yan Bindiga Na Sace Daliban Jami’a Mata…
Erinle ya ce wa’adin gidan yarin ya kamata ya gudana a bisa kai’da.
Tun da farko dai, wanda aka yanke wa hukuncin da aka gurfanar a gaban kotu, an zarge shi da kutsawa cikin babban dakin kwana na ubangidansa da nufin ya saci makullin da ake ajiya a shagon.
Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Cyriacus Osuji, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne tsakanin ranekun 4 zuwa 8 ga watan Yulin 2023, da misalin karfe 10 na safe, a gida mai lamba 6, Taiwo Osipitan Close, Parkbiew Estate-Ikoyi, Legas.
Osuji ya shaida wa kotun cewa Robson ya fasa kofa inda ya shiga gidan wani Odion Bello ya saci Laptop guda daya ta kamfanin Toshiba wanda kudinta ya kai Naira 800,000.
Ya ce, “Robson ya saci Yuro 2,000, Fam 1,000, $1000, agogon hannu na gwal guda hudu wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 4, puds wanda kudinsu ya kai Naira 450,000, ya saci kudin Katar dari takwas (800 Katar Riyal) da agogon hannu na Puma daya da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.2.
“Sauran kayayyakin da aka sace sun hada da zoben Lu’ulu’i da Abin Wuya da darajarsu ta kai Naira miliyan 100, an sace wani abin wuya da kudinsa ya kai Naira miliyan 5, da wani akwati da aka sata da kudinsa ya kai Naira 500,000, da katin kiredit da kuma katin bashi na platinum na kasar Ingila.”
Mai gabatar da kara ya ce duk kadarorin da aka sace na Bello ne wanda ya kai karar.
A yayin da yake yanke hukuncin, alkalin kotun ya yanke wa Robson hukuncin daurin watanni shida a gidan, shekaru biyu kan laifi na biyu, watanni shida kan laifi na uku, da shekara daya kan laifuka hudu zuwa shida.
Erinle ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a yari.