An dawo da zirga-zirgar jirage a filin jirgin sama na Hassan Usman Katsina, da ke Kaduna bayan da hukumomi suka dakatar da zirga-zirgar jiragen a Kaduna saboda rashin tsaro. Jirgin Air Peace ERJ-145, ya sauka a filin jirgin da misalin karfe 5:10 na yammacin ranar Litinin.
don sanar da sake dawo da zirga-zirgar jiragen sama a babban birnin jihar, tun bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen a filin tashi da saukar jiragen a watan Maris din shekarar 2022, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai musu. Fasinjoji da masu gudanar da harkokin kasuwanci a kusa da filin jirgin sun bayyana farin cikinsu da sake dawo wa da zirga-zirgar jiragen a filin jirgin amma sun yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tura karin jami’an tsaro tare da tabbatar da tsaro a ciki da wajen filin jirgin.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji Da Dama, Sun Kwato Makamai A Sokoto
- Me Ya Sa Dangantaka Da Sin Ke Samun Karbuwa A Afrika?
Shugaba mai kula da filin jirgin, Adamu Sheikh, ya ce, akwai sauran kamfanonin jiragen sama da za su fara zirga-zirga zuwa Kaduna, ya kuma ba da tabbacin cewa an samar da isasshen tsaro da kayan aiki don sauka da tashi a filin jirgin.
Mai kula da jiragen Air Peace da ke Kaduna, Fatima Ndayako ta shaida wa manema labarai cewa, “kamfanin ya dawo da zirga-zirgarsa ne Kaduna saboda yawan kiraye-kiraye da abokan cinikinmu ke yi na bukatar dawo wa.” Ta ce, Air Peace zai rika gudanar da ayyukanshi na yau da kullum daga Kaduna zuwa Legas, ta kara da cewa “a halin yanzu. , Air Peace ne kawai jirgin da ke aiki tsakanin Legas da Kaduna a filin jirgin sama na Kaduna, inda ya samar da jiragen da za su dauki fasinjoji 50 kacal.”
An tattaro cewa, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ne ya taimaka wajen dawo da ayyukan jiragen sama a jihar bayan ganawa da shugabannin kamfanonin jiragen sama a Abuja tare da ba su tabbacin daukar matakan tsaro da suka dace.