Kawo yanzu dai tuni kungiyoyin Premier League suka kashe kudi da yawa a kwana hudu a bana, an yi cinikin Fam miliyan 210.5 fiye da abin da aka kashe a watan Janairun wannan shekarar.
Kungiyoyi da yawa sun yi ciniki tun kafin ranar Lahadi, inda ranar Litinin aka sanar da wadanda aka dauka da wadanda aka sayar da kuma wadanda kungiyoyinsu ba za su kara musu sabon kwantiragi ba.
- Yadda Rangers Ta Lashe Gasar Firimiyar Nijeriya
- Yadda Aka Kafa Tarihi A Gasar Firimiyar Ingila Da Aka Kammala
To amma kungiyoyin sun yi kokarin kauce wa debe musu maki, idan ba su kashe kudi daidai samu ba, wa’adin da ya cika ranar 30 ga watan Yuni kamar yadda hukumar kula da gasar firimiya ta tsara.
Sai a ranar Juma’a 30 ga Agustan 2024 za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo, tuni kuma kungiyoyin suka tsara yin cefanen ‘yan wasa da wuri kamar yadda aka saba duk shekara.
Kungiyoyin da suka fi yin cefane tun daga ranar 14 ga watan Yuni da aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo, sun hada da Aston Billa da Eberton da Chelsea da kuma Newcastle United.
Aston Billa ta sanar da faduwa a kasuwanci na Fam miliyan 119m tun daga 31 ga watan Mayun, 2023, hakan ya sa ta cefanar da wasu ‘yan wasa don kar ta karya ka’ida kuma ta fuskanci fushin hukuma.
An kwashe maki shida a Eberton a kakar da ta wuce, bayan karya doka da ta yi har karo biyu, yayin da Chelsea ta kashe Fam biliyan daya tun bayan da Todd Boehly ya mallaki kungiyar a shekarar 2023.
Yawancin cinikin Chelsea kan kwantiragin kaka shida ta dunga yi, wadda ta dunga raba yadda take biya kudin da ta sayi dan wasa, hakan ya sa ba ta karya dokar kashe kudi daidai samu ba.
Wasu rahotannin sun ce Newcastle ta haura da Fam miliyan 50 na ka’ida a ranar Asabar da safe, hakan ya sa ta dauki mataki kafin a same ta da laifin da za a kwashe mata maki.