Kamfanonin sadarwa a Nijeriya sun fara datse kusan layukan waya miliyan 66 da ba su da aka gaza haɗa wa da Lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta.
Wannan matakin ya biyo bayan gargaɗi da ƙarin wa’adin da aka ba wa ‘yan Nijeriya don cika tsarin haɗa NIN da SIM, wanda manufarsa ita ce inganta tsaro da tantance ƴan ƙasa.
- Sin Na Matukar Adawa Da Karin Haraji Daga Gwamnatin Amurka
- Shugaban Ghana Ya Kaddamar Da Tashar Ruwa Ta Kamun Kifi Wadda Kamfanin Sin Ya Tallafa Wajen Gina Ta
Kamar yadda aka bayyana a watan Maris na shekarar 2024, an haɗa layukan waya miliyan 153 daga cikin miliyan 219 na wayar hannu da ke aiki zuwa NIN, lamarin da ya bar miliyan 66 cikin haɗarin a datse su.
Hukumar sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta riga ta datse wasu layukan wayar da ba a tantance ba a nan take a watan Yuli, wanda hakan ya haifar da mummunar wahala tsakanin ƴan ƙasa. Kamfanonin sadarwa irin su MTN, Airtel, Glo, da 9mobile sun buƙaci masu amfani da waɗannan layukan da su kammala haɗa NIN-SIM don guje wa datsewar dindindin.
Manufar haɗa NIN da SIM, wacce aka fara a shekarar 2020, na da nufin rage zamba, ta’addanci, da sauran laifuka ta hanyar buƙatar kowane layi na SIM ya kasance an haɗa da sahihiyar NIN.
Yanzu haka dai NCC ta tsaya kan wannan manufa, tare da tsayar da wa’adin ranar 15 ga Satumba, 2024, don cikakken bin doka ta tilas.