Kwamitin Raba Taimakon Ambaliyar Ruwa na Jihar Borno ya fara tantance fiye da mutane 7,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a Limanti, ƙaramar hukumar Maiduguri.
An fara tantancewa ne yau Asabar a Makarantar Firamare ta Abubakar ibn Garbai Elkanemi, bayan kammala irin wannan a tantance wa a Gwange 1, inda Gwamna Babagana Zulum ya ƙaddamar da rabon kayayyakin tallafi.
- Har Yanzu Kuɗin Taimakon Ambaliya Da Borno Ta Samu A Hannunta Bai Kai Biliyan 5 Ba
- Binani Ta Bada Tallafin Naira miliyan 50 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Borno
An fitar da sunayen mutanen da ambaliyar ta shafa a fadar dagacin yankin domin tantancewa, tare da kafa tebur na ƙorafe-ƙorafe domin magance duk wata matsala.
Shugaban kwamitin, Injiniya Baba Bukar Gujibawu, ya tabbatar wa waɗanda ambaliyar ta shafa cewa za a gudanar da aikin cikin gaskiya, tare da yin kira da su yi haƙuri, yana mai cewa za su tantance duk wanda aya cancanta.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Zulum ya raba kayayyakin tallafi ga sama da mutane 5,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a Gwange 1 ranar 24 ga Satumba, 2024.