A yau Jumma’a, an fitar da jigo da tambarin shirye-shiryen murnar bikin sabuwar shekarar Sinawa na 2025, wato bikin bazara na shekarar maciji na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG. Za a gudanar da biki bisa jigon “Kara himma a shekarar maciji” bisa yanayi na farin ciki da jin dadi, ta yadda jama’ar kasar Sin a duk fadin duniya za su yi bikin sabuwar shekara mai ban sha’awa bisa kalandar gargajiyar Sin a ranar jajibirin bikin sabuwar shekara.
Tambarin shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na bana, yana nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin shekarar maciji da kayan gargajiya na Ruyi, mai cike da kawo farin ciki ga kasar, kuma yana nuna tushen ruhi da karfin zamani na al’ummar kasar Sin.
Shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG za su kayatar tare da taya murnar sabuwar shekara ga jama’ar kasar Sin a duk fadin duniya a jajibirin sabuwar shekarar, tare da maraba da shekarar maciji mai sa jin dadi. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp