Yau Alhamis 16 ga wata ne, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya fitar da takardar bayani, game da inganta dokoki a harkokin yanar gizo ta intanet na kasar a sabon zamanin da muke ciki, inda ya yi bayani kan yadda kasar take kokarin inganta dokokin intanet, da dabaru gami da hikimomin kasar a wannan fanni.
Takardar ta ce, kasar Sin ta ayyana batun kula da harkokin yanar gizo ta intanet bisa dokoki, a matsayin wani muhimmin bangare na daidaita harkokin kasa bisa dokoki daga dukkan fannoni, da gina kasa ta hanyar raya harkokin intanet, da kokarin gina wasu ingantattun tsare-tsaren da suka shafi dokokin intanet, da sa ido kan harkokin intanet, da bada tabbacin dokoki da sauransu.
Inganta dokokin intanet da kasar Sin ta yi, ba karfafa aikin daidaita harkokin intanet na kasar take yi ba, har ma da nunawa duniya dabaru da hikimomin kasar a wannan fanni.
Takardar ta kuma ce, kasar Sin na fatan hada kai tare da ragowar kasashen duniya domin inganta dokokin da suka shafi harkokin intanet, ta yadda al’ummomin kasa da kasa, za su kara cin alfanu daga ci gaban fasahohin sadarwar zamani. (Murtala Zhang)