Jirgin sojin yaki samfarin C 130 ya debo dalibai 80, sai kuma jirgin kamfanin Air Peace ya kwaso 274.
Jiragen farko dauke da ‘yan Nijeriya da aka kwaso daga kasar Sudan sun isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Laraba.
- Sojoji Sun Kubutar Da Wasu ‘Yan Matan Chibok 2 Bayan Shekara 9 A Hannun Boko Haram
- Yadda Aka Yi Bikin Tunawa Da Ma’aikatan Kashe Gobara Na Duniya A Kano
Jimullar dalibai 354 ne jiragen suka dauko daga filin jirgin saman birnin Alkahira na Masar.
Jirgin farko ya sauka a Abuja ne da misalin karfe 2 na dare.
Manyan jami’an gwamnatin Nijeriya da suka hada da Ministar Ma’aikatar Agajin Gaggawa da Jinkai, Sadiya Farouk ne suka tarbi daliban.
A lokacin da ta ke jawabi, Hajiya Sadiya ta ce gwamnati za ta bai wa kowanne mutum N100,000 domin ya samu damar kula da kansa.
Daliban na Nijeriya sun shafe kwanaki kan iyakar Sudan da Masar sakamakon matakin da kasar ta dauka na kin bude iyakarta domin su wuce.
Sai dai bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa baki da kuma taimakon Shugaba Abdel Fattah El-Sisi na Masar, hukumomi sun bude iyakar.
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta yi kokarin dauko duk wani dan Nijeriya da ke Sudan.
Rikicin na Sudan, wanda ake yi tsakanin sojin kasar da dakarun RSF, ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da jikkata dubbai.
Kazalika rikicin ya sanya kasashen duniya suna kwashe ‘ya’yansu saboda fargabar abin da ka je ya dawo.