Shehun malami a kwalejin nazarin tattalin arziki na jami’ar Cape Town, Anthony Black, ya bayyana kyakkywan fata game da rawar da bangaren yawon bude ido na kasar Sin zai taka wajen habaka tattalin arzikin kasar.
Yayin wata hira da manema labarai, masanin kan harkokin tattalin arziki ya kuma yi ammana cewa, yadda bangaren yawon bude ido na kasar Sin ke samun tagomashi, wata babbar dama ce ga kasar Afrika ta kudu.
A cewarsa, yana da kwarin gwiwa kan sauye-sauye a bangaren tattalin arzikin Sin. Ya ce ya yi imanin tattalin arzikin wanda ingantattun fasahohin zamani ke ingiza shi, na da dimbin damarmaki. Ya kara da cewa, kamar yadda kowa ya sani, tattalin arzikin Sin na samun ci gaba cikin sauri, kuma a yanzu yana kokarin sauyawa daga mai sauri zuwa mai matukar inganci. Yana mai jadadda hakan a bangarori kamar na kirkire-kirkire da suka samar da daidaito a tattalin arzikin.
Har ila yau, ya ce yana da yakinin a wannan gaba, fadada tattalin arzikin da fasahohi masu inganci su ne mafi dacewa da kasar Sin. Inda ya ce kasar ta sanya wasu burika masu dogon zango, don haka tagomashin da za ta samu na da yawa sosai, haka ma a fannin ci gaban fasahohi. (Fa’iza Mustapha)