A daidai lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron kolin G20 karo na 19 da aka gudanar a Brazil kana da ziyarar aiki a kasar, babban rukunin gidan radiyo da talibiji na kasar Sin wato CMG ya yi bikin gabatar da shirin da ya hada, mai taken “Bayanan magabata da Xi Jinping yake so”, na 3, da harshen Porgugal, a Brasilia hedkwatar kasar Brazil a jiya Laraba. Wakilai fiye da dari 2 daga bangarorin siyasa da tattalin arziki da al’adu da kafofin yada labarai suka halarci bikin.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi a wajen bikin cewa, wannan shiri ya zabi wasu littattafai da jimloli da Xi Jinping ya ambata a cikin jawabai da sharhin da ya gabatar, wanda ya bayyana basira da al’adun Sin masu zurfi da ruhin raya kasar a sabon zamani, matakin da ya samar da wata dama mai kyau ga jama’ar kasar Brazil wajen fahimtar tunanin shugaba Xi Jinping a fannin gudanar da mulki a kasarsa. (Amina Xu)