An gano wani sabon zargin cushen kuɗi mai yawan gaske da ya kai har Naira biliyan 5 a cikin kasafin kudin Hukumar Hajjin Nijeriya (NAHCON), wanda ya haifar da kira ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su gaggauta bincikar lamarin. Wasu takardu a hukumance sun nuna cewa an saka kuɗin a ƙarƙashin shirin “Taimakon aikin Hajji” ta hannun kwamitin majalisar Dattawa kan harkokin ƙasashen waje.
Hajiya Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktan bayanai ta NAHCON, ta ce ba ta iya tabbatar da samun wasiƙar da ke nuna saka kuɗin. Kasafin kuɗin hukumar na 2025 ya kai biliyan 7.63, amma biliyan 5 daga da ake zargin ba a ware su don wani takamaiman aiki ba.
Bincike ya nuna cewa an yi irin wannan cushen kuɗin a cikin kasafin kuɗin hukumar aikin ibada ta Kiristocin Nijeriya. Wasu wasiƙu na cikin gida sun nuna cewa za a raba kuɗin tsakanin jami’an hukumar da ‘yan kwamitin majalisar dattawa, inda kwamitin ya ke da kasun biliyan 2.
Wannan ba shine karo na farko da ake zargin cushen kuɗi a NAHCON ba. A baya, an saka miliyan 382 a cikin kasafin kuɗin 2022 don ayyuka masu alamar tambaya, ciki har da siyan motoci ga ‘yan majalisa. Ma’aikatan hukumar sun bayyana cewa ba a aiwatar da waɗannan ayyukan ba.
Masu ruwa da tsaki sun yi kira ga EFCC da ICP su gudanar da bincike mai zurfi. Wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Isma’eel Muhammad Bello, ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai cewa “wannan zamba hari ne kan Musulunci”. Hukumar EFCC ta ce tana binciken wani ofishin tafiye-tafiye da ake zargin yana da hannu a zamben.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp