Akalla jihohi biyu tare da babban birnin Nijeriya, Abuja ne suka fuskanci barkewar wasu cutuka a makon da ya gabata da wanda ake ciki, al’amarin da ya tayar da hankalin al’umma da hukumomi.
Adamawa
An samu barkewar wata bakuwar cuta mai zagwanye naman jikin mutum da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai.
- Sojoji Sun Kama ‘Yan Ta’adda 25, Sun Ceto Mutum 16 Da Aka Sace
- An Shirya Bikin Kaddamar Da Shirin Gaskiya Na Talabijin “Laszlo Hudec” Cikin Harshen Slovak A Kasar Slovakia
Kaduna
Ita ma ta samu barkewar cutar da hukumomi suka ce Mashako ce wadda ta kashe yara biyu sannan ta tilasta rufe makarantun jihar.
Ita kuwa Abuja Babban Birnin Nijeriya ta samu wasu marasa lafiya guda biyu da wani nau’in zazzabi da ke sa mutane zubar da jini amma hukumomi sun ce ba a sami marasa lafiyar da Lassa ko kuma Ebola ba.
Cuta mai zagwanye naman jikin dan’adam
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, NAN ya rawaito cewa cutar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai a Jihar Adamawa tana faraway ne daga kuraje.
Daga nan kuma sai su fashe tare da zagwanyewa inda wani lokacin ma suke side fatar har su tarar da kashi a gabar da cutar ta shafa.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cutar kuraje ta Buruli Ulcer da daya daga cikin cutukan da ba a fiya mayar da kai a kansu ba a duniya.
WHO ta kuma ce cutar na barkewa a karkara musamman da ke kusa da ruwa da ke fama da rashin asibitoci.
Jami’i a shirin kasa na dakile cutar tarin fuka da kuturta a Nijeriya, Dr Adesigbin Olufemi ya sanar da cewa an samu masu dauke da cutar su 67, inda za a yi wa mutum 8 tiyata.
Olufemi wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi ya ce duk da cewa ba a gano dalilin faruwar cutar ba amma an fi zaton cewa cutar kuraje ce ta Buruli Ulcer wadda ake ci gaba da binciken gano bayanai a kanta.
Zazzabi da aman jini a Abuja
Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja ya fuskanci wata bakuwar cuta a karshen makon da ya gabata, al’amarin da ya jefa al’ummar birnin cikin razani da fargaba.
Bayanai dai sun nuna cewa an samu wasu mutum biyu da zazzabi mai tsanani tare da aman jini ta baki da hanci da ta dubura a wani asibiti da ke birnin.
Bayanai sun nuna cewa daya daga cikin mutanen ya yi bulaguro zuwa kasar Rwanda domin yawan bude idanu, inda kuma tun a Rwandar ya fara fuskantar alamun cutar.
Ba tare da bata lokaci ba sai asibitin ya sanar da hukumar da ke dakile cutuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC wadda kuma ta umarci jami’anta su yi gwaje-gwaje domin gano ko cutar na da alaka da zazzabin cutar Ebola da Marburg da Dengue da kuma na Lassa.
Tuni hukumomi ciki har da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Kano ta gargadi al’ummar jihar da su kula da shigi da ficin al’umma kasancewar jihar na da tarihin shigi da fici kasancewarta cibiyar kasuwanci.
Mashako a Kaduna
Sakamakon barkewar cutar ta mashako da ta yi sanadiyyar mutuwar yara guda biyu Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Kaduna, hukumomi sun rufe makarantu a yankin na tsawon mako guda.
Kwamishiniyar lafiya a jihar Dr. Umma Kulthum Ahmed ta ce an rufe makarantun ne saboda kauce wa karuwar yaduwar cutar a tsakanin dalibai, ganin cewar yara kanan ne suka fi kamuwa da cutar.
Fiye da mutum 40 aka killace da suka kamu da cutar sai dai daga bisani an sallami wasu da dama daga cikinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp