Masana kimiyya sun gano wani wuri da suka yi amannar shi ne daji mafi dadewa a duniya, mai dauke da wasu bishiyoyi a Kudu Maso Yammacin Ingila.
An gano shi ne a saman wani tsauni kusa da Minehead, Somerset da ke kusa da wani sansannin Butlin da ake zuwa hutu.
- Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
- An Kama Wani Matashi Mai Shekaru 25 Bisa Zargin Kashe Abokinsa A Kano
Masu bincike daga jami’ar Cambridge da Cardiff sun ce bishiyoyin da aka gano su ne mafi dakewa a Burtaniya kuma su aka sani mafi dakewa a yanzu a duniya.
An fi sanin bishiyoyin da Calamophyton tana kama da bishiyar kwakwar manja.
An kwatanta ta da bishiya mafi tsayi a duniyarmu ta yau, inda ta kai tsayin mita biyu zu-wa hudu.
Kazalika sun bayyana bishiyoyin da tsayin jijiyoyi da kuma tsari na daban.
Sun fito da bayanan yadda bishiyoyin suka taimaka wajen rike kasa, suka kuma fitar da zanen gabar tekun na tsayin daruruwan shekaru da suka gabata.
“Lokacin da na fara ganin hoton bishiyoyin nan da nan na gano yadda suke, saboda kwashe shekara 30 da na yi ina karantar irin wakannan bishiyoyin a fakin duniya,” in ji Dr Christopher Berry na makarantar nazarin kasa da kimiyyar muhalli a Cardiff.
“Abin birgewa ne ganin irin wadannan bishiyoyin a kusa da gida.
Amma abin ba da labarin shi ne yadda ake kallon su idan an kaga kai sama, kuma sun girma a wuri mai kyau.”
Dakta Paul Kenrick wanda kwararre ne a gidan tarihi na Natural History, amma ba ya cikin binciken, ya ce wannan ya bayar da haske kan yadda tsirrai ke girma tare na tsayin lokaci.
Masu binciken sun ce dajin ya girmi na New York da a baya ya fi kowanne tsufa da wajen shekara biliyan hudu.
Masu binciken sun ce yankin da aka gano dajin a baya yana yawan bushewa amma akwai hanyoyin ruwa a tare da shi, amma ba ya tare da Ingila, amma wani sashen shi na Jamus da Belgium, inda aka fi samun irin wadannan bishiyoyi.
“Wannan daji ne mai kayatarwa, ba kamar kowanne irin daji da muke gani ba a yau,” in ji Farfesa Neil Dabies na sashen kimiyyar kasa da ke Cambridge, wanda shi ne maru-bucin binciken na farko.
“Babu wata ciyawa ko wani tsiro da za mu yi magana a kan shi wanda bai bayyana ba yanzu, amma akwai wasu tsirrai da dama da suke da matukar tasiri ga kwarin kasa.”
Dakta Kenrick ya ce bishiyoyin na da banbanci daga wadanda muke gani a yau.
Wacce za a ce suna yanayi ita ce Dicksonia da ake samu a yankin antarctica, wata kalar bishiya da aka rika samu a Australiya, amma an fi ganin ta a Birtaniya.