• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Gano Dalilin Faruwar Gobarar Kasuwar Kwari A Kano

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Kano

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano ta jawo asarar miliyoyin Naira, inda ta ƙona manyan shaguna biyu kurmus.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa an gano matsalar ta samo asali ne daga fitilar wutar lantarki ta mai amfani da hasken rana (Solar) Gidan Inuwa Maimai a kan titin Bayajidda ce ta haddasa gobarar da ta tashi da misalin ƙarfe 8:00 na dare a ranar Asabar.

  • An Kama Mutum 89 Da Ake Zargi Da Fashi Da Dillancin Muggan Kwayoyi A Kano
  • Ahmad Musa Da Shehu Abdullahi Sun Koma Kano Pillars Da Taka Leda

Ko da yake gobarar ta shafi shaguna 13, aikin gaggawa da jami’an hukumar kashe gobara na kasuwar da kuma ‘yansanda suka yi ta taimaka wajen rage girman ɓarnar. An tabbatar da cewa shaguna biyu sun ƙone gaba ɗaya, yayin da wasu shaguna 11 suka samu lahani kaɗan sakamakon ruwa da aka yi amfani da shi wajen kashe gobarar. Hakazalika, an samu nasarar daƙile yunkurin ‘yan daba da suka yi ƙoƙarin yin sata a shagunan da gobarar ta shafa.

Kano

Ƙungiyar kasuwar Kantin Kwari ta yi alƙawarin ɗaukar matakan kariya don hana sake afkuwar irin wannan lamari, ciki har da cire silindar gas da masu siyar da abinci ke amfani da su da kuma janareto daga cikin kasuwar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Gobarar ta faru ne a lokacin da babu wutar lantarki, wanda hakan ya sa aka gane cewa matsalar Solar ce ta haifar da lamarin. Ƙungiyar kasuwar da hukumomi sun yi kira ga ‘yan kasuwa da su haɗa kai wajen tabbatar da tsaron muhalli ga kowa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 
Manyan Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

October 22, 2025
Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi
Manyan Labarai

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta
Da ɗumi-ɗuminsa

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Next Post
Adadin Motocin Da Suka Yi Zirga-Zirga Kan Gadar HK-Zhuhai-Macao Ta Kai Matsayin Koli A Jiya Asabar

Adadin Motocin Da Suka Yi Zirga-Zirga Kan Gadar HK-Zhuhai-Macao Ta Kai Matsayin Koli A Jiya Asabar

LABARAI MASU NASABA

Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

October 22, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

October 22, 2025
Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

October 22, 2025
Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

October 22, 2025
Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

October 22, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

October 22, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025
Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.