Wata tsohuwa mai shekaru 96 mai suna Habiba Ado ta rasu bayan faɗawa a cikin masai a Kauyen Sarai, ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da ke Jihar Kano.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ACFO Saminu Yusif, ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:27 na safe daga wani mutum mai suna Usman Adamu, wanda ya sanar da cewa wata mata ta faɗa shadda a yankin.
- Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
- Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu
A cewar Yusif, lokacin da jami’an ceto suka isa wurin daga ofishin shalƙwatar hukumar, sun gano cewa tsohuwar ta ɓata har na tsawon kwanaki huɗu, kafin daga bisani aka gano gawarta a cikin banɗakin.
Ƴan uwanta sun shaida wa jami’an hukumar cewa marigayiyar ta daɗe tana fama da cutar taɓin hankali, wanda ake zargin ya haddasa afkuwar lamarin. “Jami’anmu sun ciro ta daga ramin shaddar cikin halin suma, amma daga bisani aka tabbatar da mutuwarta,” in ji Yusif.
Ya ƙara da cewa an miƙa gawar marigayiyar ga Musa Muhammad, mai unguwar Sarai, yayin da hukumar ta yi kira ga jama’a da su rika rufe shaddar su da kyau domin kauce wa irin wannan mummunan lamari a nan gaba. Kakakin ya kuma ce Daraktan Hukumar, Alhaji Sani Anas, ya jajanta wa iyalan mamaciyar tare da tabbatar da cewa hukumar zata ci gaba da bada agajin gaggawa a dukkan sassan jihar.













