Yau Litinin, an gudanar da taron dandalin tattaunawar neman sabon tunani na asali na 2025 a birnin Hangzhou dake lardin Zhejiang. Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, Li Shulei, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.
Mahalarta taron sun bayyana cewa, ya kamata mu ci gaba da sa kaimi ga yin gyare-gyare da kirkire-kirkire yayin bunkasa al’adun gargajiya na kasar Sin, da kuma nuna kimar kasar Sin da karfin wayewar kai da al’adu. A sa’i daya kuma, kamata ya yi a horar da manyan kwararru na al’adu, da kyautata tsarin ba da kariyar tarihi da al’adu, don kare albarkatun al’adun kasar Sin.(Safiyah Ma)












