An gudanar da taron tattaunawa na kasa da kasa mai taken “Sin a yanayin bazara: Kasa da kasa suna cin gajiyar damammakin Sin”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya shirya a birnin Ankara dake Turkiya.
Yayin taron da ya gudana a ranar 12 ga watan nan, mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban CMG Shen Haixong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
- MOFA: Ya Kamata G7 Ya Mai Da Hankali Kan Habaka Hadin Kai Da Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa
- Matatar Dangote Ta Dakatar Da Sayar Da Man Fetur A Naira
Shen Haixong, ya ce Sin ba za ta iya samun ci gaba ba idan ta bar tafiya tare da sassan kasa da kasa, kuma ci gaban kasa da kasa yana bukatar kasar Sin. Ya kara da cewa, CMG na fatan yin amfani da fa’idarsa ta watsa labarai ta hanyar cuduanya, da kirkire-kirkiren kimiya da fasaha dake kan gaba a duniya, don raba dammamakin ci gaba na zamanantarwa irin ta Sin tare da abokai na kasa da kasa.
Baki mahalarta taron daga bangarorin siyasa, da kasuwanci, da ilmi da wakilan kafofin watsa labarai fiye da 150, ciki har da shugaban kungiyar abokantakar Turkiya da Sin Mista Mehmet Şükrü Koçoğlu, sun halarci taron, inda suka gudanar da tattaunawa bisa jigon “Dammakin da ci gaban Sin mai inganci ya kawo wa duniya” da dai sauransu.
A ranar 14 ga watan Maris, an gudanar da taron tattaunawa na kasa da kasa mai taken “Sin a yanayin bazara: Kasa da kasa suna cin gajiyar damammakin Sin” a Bogotá, hedkwatar Colombia. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp