Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, sanarwar hadin gwiwa da kuma sanarwar tsaro da wadata a teku da taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 ya fitar, sun gurbata da karkatar da gaskiya. Kasar Sin ta bukaci kungiyar G7 da ta daina yi wa ‘yancin kasar zagon kasa, da tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da haifar da rikici da adawa ta hanyar kungiyanci, a maimakon haka, ta kara yin kokari wajen inganta hadin kai da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya.
Kalaman na baya-bayan nan da kungiyar G7 ta fitar sun sake tabo batutuwan da suka shafi kasar Sin, inda suka yi tsokaci kan batun Taiwan, da harkokin teku, da kuma nuna damuwarsu cewar kasar Sin na samarwa kasar Rasha makamai da kuma kayayyaki masu amfani biyu.
- Layin Dogo Na Habasha-Djibouti Na Habaka Kasuwanci Da Karfafa Hada-hadar Kayayyaki
- Tattalin Arzikin Ghana Ya Bunkasa Da Kashi 5.7 A Shekarar 2024
Da take mayar da martani kan wannan batu, Mao Ning ta jaddada cewa, batun Taiwan muhimmin batu ne kasar Sin, wanda kasashen waje ba su isa su tsoma baki a ciki ba. Ta ci gaba da cewa, yanayin tekun kudancin kasar Sin baki daya na cikin kwanciyar hankali, kuma babu wata matsala da ta shafi ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da zirga-zirgar jiragen sama. G7 ya kamata ta daina tada hankali da tada husuma.
Dangane da rikicin kasar Ukraine kuwa, Mao Ning ta sake nanata cewa, kasar Sin ta ci gaba da ba da shawarar samar da zaman lafiya da yin tattaunawa, kuma ba ta taba bayar da muggan makamai ga wani bangare da ke cikin rikicin ba, kana ta tsaurara matakan hana fitar da kayayyaki masu amfani biyu. A karshe ta jaddada cewa, kasar Sin ta yi watsi da duk wani yunkuri na G7 na dora mata laifi don ta kaucewa nauyin dake bisa wuyanta. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp