Dakataccen Gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya isa babbar kotun tarayya da ke Legas domin gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ne suka gurfanar da Emefiele a gaban kotu da misalin karfe 9:20 na safiyar ranar Talata.
- Cire Tallafin Mai: NIS Ta Samar Da Motoci Kyauta Don Sufurin Ma’aikatanta
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Boko Haram Kan Zargin Shirin Kai Hari Gidan Atiku
Za a gurfanar da shi a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo bisa tuhume-tuhume biyu na mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.
A ranar 13 ga watan Yulin 2023 ne, gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban kotu kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da safarar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba kan gwamnan CBN da aka dakatar.
Gwamnatin Tarayya ta zargi Emefiele da mallakar bindiga mai lamba JOJEFF MAGNUM 8371 ba tare da lasisi ba.
Gwamnati ta ci gaba da cewa laifukan sun saba wa sashe na 4 na dokar mallakar bindiga karkashin sashe F28 da sashe na 27 (1b) na Dokokin Tarayya ma 2004.
An kuma tuhumi Emefiele da mallakar wasu harsasai ba tare da lasisi ba, wanda hakan ya saba wa sashe na 8 na dokar mallakar bindigogi F28 na tarayya na shekarar 2004 da kuma sashe na 27 (1) (b) (il) na wannan dokar.
Tun ranar 10 ga watan Yuni ne dai Emefiele ke hannun DSS inda ake ci gaba da bincike a kansa bayan dakatar da shi.