A ranar Litinin ne rundunar ‘yansandan ta gurfanar da wani mai ba da shawara kan harkokin ilimi na jami’ar Tai Solarin Sadiku Rasaki na bogi, mai shekaru 47 a gaban kuliya, da laifin karbar kudi Naira 600,000 daga hannun mahaifin wani dalibin makarantar.
An gurfanar da Rasaki a gaban kotun majistare da ke Igbosere da ke Ebute-Metta, a kan laifuka uku da suka hada da karba, sata, wanda ‘yan sanda suka ambata masa.
- Mu Kare Daraja Muhallinmu, Kuma Mu Kare Nijeriya Daga Labaran Bogi – Minista
- JAMB Ta Bankaɗo Ɗalibai 3000 Da Suka Kammala Karatun Bogi
Dansanda mai gabatar da kara, sufeta Cyriacus Osuji, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a wani lokaci a watan Satumban 2023, a Legas.
Ya ce, Rasaki, wanda ake zargin ya karbi kudi Naira 600,000, daga hannun wani Mista James Oyeleke, bisa zargin taimakawa dansa, Nathaniel Oyeleke, wajen saukaka sakin takardar shaidar makarantarsa.
Osuji ya ce kudaden da aka karba mallakin mahaifin dalibin Jami’ar ilimi ce ta Tai Solarin, Mista Oyeleke.
Mai gabatar da kara ya ci gaba da shaida wa kotun cewa Rasaki ya kwaikwayi hanyar gabatar da kansa ga wanda ya shigar da karar a matsayin mai ba da shawara kan ilimi ga jami’ar.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan da aka aikata sun sabawa sashe na 314 da kuma hukunci a karkashin sashe na 287 da 383 na dokokin laifuka na Jihar Legas 2015.
Rasaki ya musanta zargin da ake masa.
Sai dai alkalin kotun mai shari’a Oluwatosin Erinle ya bayar da belinsa a kan kudi Naira 300,000, tare da mutum biyu da za su tsaya masa.
Kotun ta ce dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya zama mutum dan uwa ne na jini, kuma ya nuna shaidar biyan haraji ga gwamnatin Jihar Legas, takardar banki na watanni shida.
Alkalin kotun ya kuma ba da umarnin a tantance adireshin wadanda za su tsaya masu.
An dage sauraron karar har zuwa ranar 30 ga Yuli, 2024, don ci gaba da zaman.