Wasu mazauna a yankin Utar Pradesh sun ga wani abin al’jabi da ba kasafai suka saba gani gani ya faru a tarihi ba.
Lamarin da ya cika su da mamaki inda aka haifi wani yaro da kafafu hudu da hannaye hudu. Tun daga lokacin ne aka yi tururuwa domin ganin lafiyar jaririn da ba’a saba gani ba.
Haihuwar jaririn ta haifarda bayan yada labarunsa, wanda hakan ya sanya al’ummar kasar Indiya yin tururuwa domin zuwa ganin jaririn.
Tun daga lokacin ne aka ayyana haihuwar yaron a matsayin wata Karama ta musamman. Yayin da ake nuna yaron da aka haifa a karshen mako a Hardol a Arewacin kasar, tare da tare da karin kafafu hudu a cikin ciki, mutane sun cika da mamaki.
Yaron da ba’a bayyana sunansa ba yana da nauyin 6.5lbs, kuma an haife shi a cibiyar kiwon lafiyar jama’a ta Shahabad, a cikin Jihar Uttar Pradesh kamar yadda gidan rediyon kasar ya bayyana. Mum Kareena, wacce ba ta bayyana sunanta na gaskiya ba an yi hanzarin garzaya da ita asibiti tun bayan fama da ciwon nakuda da a ranar Asabar 2 ga Yuli, inda kai ta asibitin ke da wuya ta haihu.
Babban al’ajabin shi ne, uwa da jaririn duk suna ciki koshin lafiya, kuma suna da kyau duk da karancin magani.
Kazalika wasu rahotanni sun ce mutane sun yi ta yin tururwa zuwa kallonsa bayan da labarin ya bazu ko ina cikin gari, sannan mazauna yankin sun bayyana lamarin kwatankwacin wata baiwa ta Allah mai kafafuwa da dama.
Wannan dai ba shi karo farko da ake tururuwa wajen zuwa kallon yaro a Kasar Indiya saboda haifarsa da wata bakuwar halitta ba, a farkon wannan shekarar, ‘yan kasar sun yi wa wani jariri da aka haifa da hannuwa da kafafuwa tsafi bayan da suka yi tunanin yana dangantaka da abin bauta. Mahaifiyar jaririn ta ga turuwar jama’a masu zuwa kallon da ta haifa a asibitin kasar dake Gabashin kasar bayan da ta haihu ranar Talata.