Wata majiya daga Jami’an tsaro, a ranar Laraba, ta bayyana cewa an sauya sojojin dake kula da gefen garin kuje da Gidan Fursunan wadanda suka son kan yanayin yankin sosai, an maye gurbin su da sabbin jami’ai, sa’o’i 24 kafin ‘yan ta’adda su kai hari gidan yarin Kuje.
Majiyar ta ce, ta yi mamakin dalilin da ya sa aka kwashe jami’an da suka kware da sanin garin sa’o’i 24, ba a kai ga kawo wasu sabbi ba, ‘yan ta’addan suka far wa yankin.
Sai dai kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, tace an sanar da ita cewa, wa’adin da ya kamata sojojin su zauna a wannan aikin ya wuce, suna bukatar sauya su da wasu.
A halin da ake ciki, majiyoyin tsaro sun shaidawa Vanguard cewa ‘yan ta’addan sun samu nasarar doke shingayen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka dasa a hanyar shiga yankin.