A jiya ne, aka kaddamar da gasar zakulo matasan Afirka da suka yi fice a fannin fasaha karo na 8 (ATC), gasar da kamfanin AVIC na kasar Sin ya dauki nauyin shiryawa a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, a ci gaba da kokarin inganta fasahohi da kasuwanci na matasan nahiyar.
Sama da matasa 70 daga kasashen Kenya da Uganda da Tanzania da Ghana da Masar da Cote d’Ivoire da Zambia da kuma Zimbabwe ne, za su halarci shirin na tsawon wata guda, a wani mataki na bunkasa kwarewarsu wajen amfani da fasahohin da suka shafi gine-gine.
Gasar mai taken “Rawar da aikin injiniya yake takawa wajen bunkasa masana’antu a Afirka,” shirin na ATC na wannan shekara, zai koyar da ‘yan takara manyan fasahohin gine-gine kamar zane-zanen kwamfuta da na na’urorin zamani.
Wadanda suka yi nasara a gasar, wadda jami’ar fasaha ta kasar Kenya za ta dauki nauyinsu, za su samu kyaututtuka na kudi, da takardun shaida, har ma da kudin tallafin karatu a jami’o’in kasar Sin. (Mai fassara: Ibrahim)