Hukumar bunkasa ci gaba, da gudanar da sauye-sauye ta lardin Liaoning na arewa maso gabashin kasar Sin, ta kaddamar da ginin cibiyoyi 10, na samar da makamashin lantarki daga karfin hasken rana da iska, aikin da zai lashe kudin Sin har sama da yuan biliyan 6, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 883.9.
A cewar hukumar, za a gina cibiyoyin ne a biranen Shenyang, da Dalian, da Dandong, da Yingkou da Chaoyang. Kuma bayan kammalar su, adadin jimillar lantarkin da za su samar zai kai sama da kilowatt/sa’a biliyan 2.2, adadin da zai biya bukatun lantarki ga iyalai miliyan 2 a shekara guda. Kaza lika a duk shekara, aikin zai rage amfani da kwal har tan 675,700, tare da rage fitar da iska mai gurbata yanayi har sama da tan miliyan 2.
Aikin wani bangare ne na hadin gwiwar gwamnatin lardin na Liaoning, da kamfanin China Huaneng. Ana kuma sa ran zai jawo jarin da ya kai sama da yuan biliyan 100 ga lardin, karkashin manufar nan ta bunkasa kasa ta shekaru biyar-biyar karo na 14, wadda Sin ke gudanarwa tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, wanda kuma ake hasashen hakan zai fadada jarin masana’antun dake da nasaba da hakan, da sama da kudin Sin yuan biliyan 50. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp