ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kaddamar Da Kungiyar Samar Da Tsarin Ci Gaban Jihar Kano

by Abba Ibrahim Wada
3 years ago
Kano

Wasu masu kishin Jihar Kano sun kaddamar da wata kungiya mai suna “Kano Charter” wadda za ta dinga bibiya tare da sanya ido a kan bukatun da al’ummar Jihar Kano suke da su na ci gaba da bunkasar tattalin aziki.

A yayin taron kaddamar da kungiyar wanda aka yi a Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma (CITAD) da ke Kano ya samu halartar manyan mutane masu kishin Jihar Kano daga fannoni daban-daban na fadin jihar.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Kammala Aikin Gadar Neja Ta Biyu
  • Yobe Ta Arewa: Machina Ya Sake Samun Nasara Yayin Da Kotu Ta Kori Karar Da Aka Sake Shigarwa A Kansa 

A jawabinsa, Dokta Isa Ahmed, wanda shi ne shugaban gamayyar, ya bayyana cewa wannan sabon tsari ne da aka shigo da shi domin ganin an dora Jihar Kano a kan turba mai dorewa duk da cewa a shekarun baya ma akwai irin wannan gamayyar.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa Kano gari ne mai cike da tarin albarkatu daban-daban saboda haka akwai bukatar samun tsari mai inganci wanda zai dora duk shugaban da zai zo a kan tsarin da zai kawo ci gaba mai dorewa a jihar.

Shi ma a yayin da yake jawabinsa, Farfesa Nu’uman Habib Muhammad da ke Jami’ar Bayero ta Kano, ya bayyana cewa dole sai an samu shugaban da zai kasance mai cikakkiyar biyayya da girmama tanade-tanaden tsarin mulki na kasa da addini da wanda zai samar da cin gashin kai da bangarorin shari’a da bijro da tsari mai saukin aiwatarwa.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Sannan ya ce Kano tana bukatar samar da hanyoyin kudin shiga da fitar da tsarin kyautata rayuwar al’umma samar da tsarin rage kashe kudaden al’umma da kuma biyayya ga tsare-tsaren kundin mulkin kasa.

Taron ya samu halartar shugaban Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa da Ci Gaban Al’umma  (CITAD), Injinya Yunusa Zakari Ya’u da Prof. Baffa Aliyu Umar da Dokta Gausu Ahmad da Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa da Dokta Bala Muhammad (Adaidaita Sahu) da Dokta Dalhatu Sani Yola da Farouk Lawal Yola da Nasidi Abdullahi da Ibrahim Ado Kurawa da Farouk Ibrahim Mukhtar da Umar Muhammad Jalo da Ibrahim Sadauki Kabara da Aliyu Isma’il diso da Tafada A. Babba da Ummi Tanko Yakasai da Amina Aminu Dantata da Auwalu Muhammad Umar da Nura Shafi’u da kuma Idris Makama Unguwar Gini da sauransu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Ambaliyar Ruwa: Ku Kwashe Jama’ar Da Suke Zaune A Yankunan Magudanun Ruwa — Sadiya Farouq

Ambaliyar Ruwa: Ku Kwashe Jama'ar Da Suke Zaune A Yankunan Magudanun Ruwa — Sadiya Farouq

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.