An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniya da bude cibiyar kiwon lafiya ta hadin gwiwa ta farko tsakanin Sin da Afirka jiya Laraba a asibitin abota na Sin da Guinea dake Conakry, babban birnin Guinea.
Shen Hongbing, mataimakin darektan hukumar kula da lafiya ta kasar Sin kuma shugaban hukumar kula da rigakafin cututtuka ta kasar, da Oumar Diouhé Bah, ministan lafiya na Guinea, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin hukumar kula da lafiya ta Jamhuriyar Jama’ar Sin da ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Guinea, kan gina cibiyar kiwon lafiya ta hadin gwiwa ta Sin da Afirka.
Yarjejeniyar tana da nufin daidaita bukatun bunkasa bangaren lafiya na Guinea, tare da tallafawa cibiyoyin kiwon lafiya da abin ya shafa daga birnin Beijing na Sin da asibitin abota na Sin da Guinea, wajen gina cibiyar kiwon lafiya ta hadin gwiwa ta Sin da Afirka (Guinea) .
Ta hanyar gabatar da fasahohi da horar da kwararru da sauransu, za a gina asibitin abota na Sin da Guinea zuwa wata cibiyar kiwon lafiya ta hadin gwiwa a fannonin bincike da jinyar cututtukan zuciya da kwakwalwa da magudanar jini, da tiyata ta amfani da fasahohin zamani, da kuma bincike da jinya ta hanyar fasahar AI.
Sannan, mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin Liu Guozhong wanda ya kai ziyarar aiki a Guinea daga ran 10 Litinin zuwa ran 12 Laraba ga wata , ya ce a shirye Sin take ta karfafa dadaddiyar abotar dake tsakaninta da kasar Guinea, da inganta goyon bayan juna da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu. Mr. Liu ya kuma halarci bikin kaddamar da mahakar karafa ta Simandou, a matsayin wakili na musammam na shugaban Xi Jinping. (Masu fassara: Safiyah Ma, Fa’iza Mustapha)














