Kasar New Zealand ta zartar da dokar hana shan taba sigari daga shekara mai zuwa a fadin kasar.
An rawaito cewa, dokar da majalisar dokokin kasar ta zartar a ranar Talata ta nuna cewa duk wanda aka haifa bayan shekarar 2008 ba zai taba samun damar siyan taba ko sigari ba.
- Kasan Wadanda Suka Kawo Boko Haram, Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Atiku
- Kotu Ta Yanke Wa Mutum 3 Hukuncin Kisa Kan Yi Wa Dalibar Jami’a Fyade
Wato adadin mutanen da ke da hanyar siyan taba zai ragu sosai a kowace shekara.
Ministar lafiya ta New Zealand, Dakta Ayesha Verrall, wacce ta gabatar da kudirin, ta ce wannan mataki ne “zama makoma mai kyau ga masu shan sigari”.
Ta kara da cewa an tsara kudirin dokar ne domin takaita yawan masu siyar da taba sigari zuwa 600 a duk fadin kasar – kasa da 6,000 a halin yanzu – da kuma rage yawan sinadarin nicotine da ke cikin sigari don rage sha’awarta.
A cewar ministar lafiyar dubunnan mutane a kasar za su kara tsawon rai da lafiya.
Kididdigar baya-bayan nan da gwamnati ta fitar a New Zealand ta nuna cewa yawan shan taba sigari ya riga ya ragu a tarihi, inda kashi 8% na manya ke shan taba kowace rana a bana, ya ragu daga kashi 9.4% a bara.