Rundunar ’Yansandan Jihar Kano, ta kama wasu matasa biyu, Mohammed Isma’il (Linga) da Sani Abdulsalam (Guchi), bisa zargin nuna makamai da kuma tayar da hankali a cikin wani bidiyo da suka wallafa a shafukan sada zumunta.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a ranar Laraba an kama su a yankin Dala bayan wani samame da aka shirya ta hanyar leƙen asiri.
- ’Yansanda Sun Ceto Mutane 16 Da Aka Sace A Edo
- ADC Tana Da Damar Kayar Da Tinubu A Zaɓen 2027 – Amaechi
An gano cewa suna tara matasa sannan suna saka bidiyo a TikTok da Facebook suna nuna makamai.
Lokacin da aka cafke su, ’yansanda sun samu takobi guda ɗaya da sanduna guda biyu a hannunsu.
Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci a gudanar da bincike a kansu.
Ya kuma gargaɗi jama’a cewa duk wanda aka kama yana amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa tarzoma ko ta’addanci, za a kama shi tare da gurfanar da shi a kotu.
Rundunar ta yi kira ga iyaye da su ja kunnen ’ya’yansu ka da suke kwaikwayon irin wannan hali ko sauran laifuka.
Ta jaddada cewa ba za ta yadda da duk wani abu da zai kawo tashin hankali a jihar ba.
Rundunar ta kuma gode wa jama’a bisa irin bayanan da suka bayar da ya taimaka wajen kama matasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp