Jami’an ‘yansanda a jihar Kaduna sun kama wasu mutane takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da fashi da makami. An kama wadanda ake zargin ne a wani samame da aka kai maboyarsu a gonar Nuba a ranar 17 ga Nuwamba, 2023.
Wadanda ake zargin sun hada da Bello Suleiman, Ismail Abubakar, Usman Suleiman, Umar Suleiman Gero, Isah Lawal, Abubakar Bello, Ibrahim Mu’azu da kuma Umar Sulaiman. Dukkanin wadanda ake zargin sun fito ne daga kauyen Farin Kasa da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.
- Da Ɗumi-Ɗumi: Jam’iyyar APC Ta Kori Shugabanta Na Jihar Bauchi, Aliyu Misau
- Rikicin Yola: Ba Yaki Mu Ke Yi Da Sojoji Ba – Sufeton ‘Yansanda
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), ASP Munsur Hassan ya fitar, ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin suna da hannu wajen yin garkuwa da Hon. Kawu Ibrahim Yakasai a ranar 25 ga Agusta, 2023. Ana kuma zarginsu da yin garkuwa da Adamu Mu’azu na kauyen Bagaldi a kwanakin baya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, akwai shugaban tawagar wanda ake yi wa lakabi da ‘Hanazuwa na kauyen Farin Kasa’, bai shigo hannu ba amma ana nan ana bibiyarsa. Rundunar ‘yansandan ta bayar da tabbacin cewa za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Kaduna, CP Musa Yusuf Garba, ya yabawa ‘yansandan bisa kokarin da suke yi, ya kuma bukace su da su kara bada muhimma kan ayyukansu na yau da kullum musamman ma lokacin bukukuwan Kirismati da na karshen shekara da ke karatowa.