Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai, UEFA ta sanar da sauye-sauyen da za a yi a gasar cin kofin zakarun Turai daga kakar wasa mai zuwa bayan daukar shekara da shekaru ana shirye-shirye.
Muhimmin sauyi da kwamitin zartarwa na UEFA ya sanar shi ne ficewa daga tsarin matakin rukuni da ake yi yanzu sannan a halin yanzu matakin rukuni na gasar zakarun Turai ya kunshi kungiyoyi 32 da aka raba cikin rukunai takwas inda kowanne rukuni ke kunshe da kungiyoyi hudu. Daga kakar wasa ta 2024/25, kungiyoyi 36 ne za su shiga gasar cin kofin zakarun Turai (tsohon matakin rukuni), wanda zai ba wa wasu kungiyoyi hudu damar fafatawa da kungiyoyin da suka fi fice a Turai.
- Ba Za Mu Lamunci Cin Zarafin Wani Da Sunan Tafsiri Ba – Gwamnatin Kaduna
- Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Tallafawa Matakan Siyasa A Sudan
Kungiyoyi 36 ne za su shiga gasar Lig guda daya wadda dukkanin kungiyoyin za su kasance a teburi daya, sannan a karkashin sabon tsarin, kungiyoyi za su buga wasanni takwas a sabon matakin gasar (tsohon matakin rukuni).
Za su fafata da kungiyoyi daban-daban guda takwas, inda za su buga rabin wadannan wasannin a gida, rabinsu kuma a waje. Domin tantance kungiyoyin da za su fafata da juna, da farko za a sanya kungiyoyin a cikin tukwane guda hudu sannan za a fitar da kowace kungiya domin ta yi wasa da abokan hamayya biyu daga kowacce tukunya, inda za a yi wasa daya da kungiya daga kowace tukunya a gida, daya kuma a waje.
Kungiyoyi takwas na farko a teburin za su tsallaka zuwa zagaye na 16 kai tsaye, yayin da kungiyoyin da suka kare a matsayi na 9 zuwa na 24 za su fafata a cike gurbi don samun damar ketarawa zuwa zagaye na ‘yan 16 na karshe a gasar sai kungiyoyin da suka kare a matsayi na 25 zuwa kasa za a fitar da su, ba tare da samun damar shiga gasar Europa League ba.