A yau Talata aka kammala taron tattauna batutuwan tsaro na kasa da kasa na Xiangshan a nan birnin Beijing. Taron na yini biyu ya samu mahalarta sama da 1,800 ciki har da mambobin tawagogi 99 da ministocin tsaron kasashe 19 da manyan hafsoshin tsaro da wakilan hukumomin kasa da kasa da masana da malamai da ‘yan kallo daga kasashe daban daban.
Yayin taron na bana mai taken “Tsaro Na Bai Daya, Zaman Lafiya Mai Dorewa”, mahalarta sun tattauna tare da musayar ra’ayi kan batutuwa da dama kamar hakkin dake wuyan manyan kasashe da hadin kan duniya kan tsaro da rawar da kasashe masu tasowa za su taka kan tsaron duniya da tsarin tsaro na yankin Asiya da tekun Pasifik da kuma tsaron yankuna da ci gabansu. (Fa’iza Mustapha)