An sake sako biyar daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga Maris, 2022.
Daga cikin fasinjojin da aka ceto akwai Farfesa Mustapha Umar Imam, likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodio (UDUS), Sokoto.
Imam ya samu rauni daga harbin bindiga a kafadarsa, lamarin ana jin tsoron ya haifar da damuwa game da lafiyarsa.
Sauran fasinjojin da aka sako sun hada da Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Muktar Shuaibu da Sidi Aminu Sharif.
Mawallafin labarai da ke zaune a Kaduna, Tukur Mamu, wanda da kansa ya tsunduma cikin tattaunawa don ganin an sako wadanda lamarin ya rutsa da su amma ya ja da baya saboda barazanar da ake yi masa a rayuwarsa ya tabbatar da sakin su ga jaridar Daily trust a ranar Talata.
Cikakkun bayanai daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp